Kafofin yanar gizo da dama sun yi kokarin tsakuro bayanai akan garin Birnin Zauma da ke karamar hukumar mulki ta Bukkuyum a jihar Zamfara amma hakar su ba ta cimma ruwa ba saboda dogara da bayanan da suka samo ta tauraron dan adam. Wasu daga cikin wadannan kafofin duniyar gizon sune www.maplandia.com, http://www.fallingrain.com da http://wikimapia.org/30372081/Birnin-Zauma wadanda sun ba da bayanan da suka takaitu akan taswira da nisan wurare. A dalilin haka na tallafawa wadannan shafukan duniyar gizon da bayanai masu fa'idar gaske akan wannan wannan gari mai dimbin tarihi. Domin fadada wannan aiki zan samar da ingantattun bayanai akan wannan gari mai dimbin tarihi ta hanyar abinda na gani da ido da kuma bayanan kunne-ya-girmi-kaka akan tarihi, al'ada da daukacin rayuwar mutanen Zauma. Kamar yadda masu karatu zasu iya gani a gefen hagu hoton ganuwar Birnin Zauma ce ta bangaren yamma. Don karin bayani masu karatu na iya tuntuba ta ta shafin Facebook a wannan madannar rariyar likau www.facebook.com/Ibrahimzauma.BIRNIN ZAUMA
Friday, August 26, 2016
BAYANI AKAN GARIN BIRNIN ZAUMA
Kafofin yanar gizo da dama sun yi kokarin tsakuro bayanai akan garin Birnin Zauma da ke karamar hukumar mulki ta Bukkuyum a jihar Zamfara amma hakar su ba ta cimma ruwa ba saboda dogara da bayanan da suka samo ta tauraron dan adam. Wasu daga cikin wadannan kafofin duniyar gizon sune www.maplandia.com, http://www.fallingrain.com da http://wikimapia.org/30372081/Birnin-Zauma wadanda sun ba da bayanan da suka takaitu akan taswira da nisan wurare. A dalilin haka na tallafawa wadannan shafukan duniyar gizon da bayanai masu fa'idar gaske akan wannan wannan gari mai dimbin tarihi. Domin fadada wannan aiki zan samar da ingantattun bayanai akan wannan gari mai dimbin tarihi ta hanyar abinda na gani da ido da kuma bayanan kunne-ya-girmi-kaka akan tarihi, al'ada da daukacin rayuwar mutanen Zauma. Kamar yadda masu karatu zasu iya gani a gefen hagu hoton ganuwar Birnin Zauma ce ta bangaren yamma. Don karin bayani masu karatu na iya tuntuba ta ta shafin Facebook a wannan madannar rariyar likau www.facebook.com/Ibrahimzauma.Friday, August 12, 2016
TARIHIN GARIN BIRNIN ZAUMA
Kwakkwarar majiya da tabbatattun bayanan tarihi sun nuna cewa an kafa garin Birnin Zauma tun kimanin shekaru fiye da 350 da suka wuce watau tun shekara 1084 AH (1663 CE) akan kididdigar da aka gina akan kintace mai karfi. Wannan kiyasi ya jingina akan tarihin zuwan Shehu Usmanu Danfodiyo wannan gari shekaru kadan kafin yakin Kwatto watau a shekarar 1804 CE inda a lokacin ya tarar da garin Zauma cike da mutane wanda a dalilin haka ya gina masallaci babba a garin. Wannan na nuna cewa koda Mujaddadi Shehu Usmanu yayi wannan rangadi, Zauma ta dade da kafuwa da shekarun da basu kasa 150 ba. Littafen "Mazan Jiya" fassarar "Great Lives" wanda Hukumar Ilimi ta Jahar Sokoto ta wallafa yayi bayani akan zayarar Shehu Usmanu a garuruwan Birnin Zauma da Zugu.Sunday, February 3, 2013
Subscribe to:
Posts (Atom)





