Kwakkwarar majiya da tabbatattun bayanan tarihi sun nuna cewa an kafa garin Birnin Zauma tun kimanin shekaru fiye da 350 da suka wuce watau tun shekara 1084 AH (1663 CE) akan kididdigar da aka gina akan kintace mai karfi. Wannan kiyasi ya jingina akan tarihin zuwan Shehu Usmanu Danfodiyo wannan gari shekaru kadan kafin yakin Kwatto watau a shekarar 1804 CE inda a lokacin ya tarar da garin Zauma cike da mutane wanda a dalilin haka ya gina masallaci babba a garin. Wannan na nuna cewa koda Mujaddadi Shehu Usmanu yayi wannan rangadi, Zauma ta dade da kafuwa da shekarun da basu kasa 150 ba. Littafen "Mazan Jiya" fassarar "Great Lives" wanda Hukumar Ilimi ta Jahar Sokoto ta wallafa yayi bayani akan zayarar Shehu Usmanu a garuruwan Birnin Zauma da Zugu.Friday, August 12, 2016
TARIHIN GARIN BIRNIN ZAUMA
Kwakkwarar majiya da tabbatattun bayanan tarihi sun nuna cewa an kafa garin Birnin Zauma tun kimanin shekaru fiye da 350 da suka wuce watau tun shekara 1084 AH (1663 CE) akan kididdigar da aka gina akan kintace mai karfi. Wannan kiyasi ya jingina akan tarihin zuwan Shehu Usmanu Danfodiyo wannan gari shekaru kadan kafin yakin Kwatto watau a shekarar 1804 CE inda a lokacin ya tarar da garin Zauma cike da mutane wanda a dalilin haka ya gina masallaci babba a garin. Wannan na nuna cewa koda Mujaddadi Shehu Usmanu yayi wannan rangadi, Zauma ta dade da kafuwa da shekarun da basu kasa 150 ba. Littafen "Mazan Jiya" fassarar "Great Lives" wanda Hukumar Ilimi ta Jahar Sokoto ta wallafa yayi bayani akan zayarar Shehu Usmanu a garuruwan Birnin Zauma da Zugu.
Subscribe to:
Post Comments (Atom)
No comments:
Post a Comment